20 Agusta 2021 - 15:15
Sojojin Siriya Sun Kakkaɓo Wasu Makamai Masu Linzamin ‘Isra’ila’ A Damaskus Da Homs

Sojojin Siriya sun sami nasarar kakkaɓo mafi yawa daga cikin makamai masu linzami da haramtacciyar ƙasar Isra’ila ta harbo su kan babban birnin ƙasar, Damaskus da kuma garin Homs da ke yammacin ƙasar, a ci gaba da wuce gona da iri da ‘Isra’ilan’ take yi kan ƙasar Siriya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : Rahotanni sun ce ‘Isra’ilan’ dai ta kai waɗannan hare-hare ne da safiyar yau Juma’a kamar yadda tashar nan ta Al-Mayadeen ta ƙasar Labanon ta bayyana inda ta ce baya ga birnin na Damaskus har ila yau Isra’ilan ta kai hari garin Homs da ke yammacin ƙasar.

Har ila yau rahotannin sun ce an ji ƙarar fashewar wasu abubuwa a birnin na Damaskus bayan da makaman kariya na ƙasar Siriyan a yayin da suke harbo makamai masu linzamin Isra’ilan da suka shigo cikin birnin.

Kafafen watsa labaran Isra’ilan ma sun tabbatar da kai waɗannan hare-hare kan birnin na Damaskus.

Tashar talabijin ɗin Al-Mayadeen ɗin tace sojojin Siriyan sun sami nasarar kakkaɓo mafi yawa daga cikin makamai masu linzamin da Isra’ilan ta harbo.

Ma’aikatar tsaron ƙasar Siriyan dai ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike kan wannan wuce gona da iri na Isra’ilan.

342/